IQNA

An Zanga-Zangar Neman Sulhu A Yankin Rakhine Na Myanmar

16:54 - October 11, 2017
Lambar Labari: 3481991
Bangaren kasa da kasa, dubban mutane suka gudanar da jerin gwano a kasar Myanmar domin yin kira da a samu sulhu a yankin Rakhine.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na channelnewsasia cewa, fiye da mutane dubu talatin ne suka gudanar da jerin gwano a kasar Myanmar domin yin kira da a samu sulhu a yankin Rakhine na mabiya addinin muslunci.

Babbar manufar jerin gwanon dai ita ce yin kira ga mahukuntan kasar ad su dauki matakan da suka kamata domin ganin an kawo karshen tashin hankalin da yake faruwa a yankin na Rakhine wanda musulmi da dama suke zaune a cikinsa.

Wannan gangami dai ya hada da mabiya addinin buda da kuma kiristoci da ma musulmi wadanda dukakninsu ba su amince da abin gwamnatin kasar tare da masu tsatsauran ra'ayin addinin buda na kasar suke yi ban a kisan msuulmi 'yan kabilar Rohinya.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da daman a duniya sun bukaci da a gudanar da sahihin bincike kan kisan da ake yi wa msuulmi a kasar, amma manyan kasashe ba bayar da muhimmanci ga lamarin ba.

Fiye ad musulmi dubu uku ne aka tabbatar da cewa an kasha Myanmar a cikin 'yan makonnin da suka gaba a hannun dakarun kasar da yan addinin buda masu tsatsauran ra'ayi.

3651712


captcha