IQNA

Majalisar Musulmin Kenya Ba Za Ta goyi Bayan Wani dan Takara Ba

22:51 - October 18, 2017
Lambar Labari: 3482012
Bangaren kasa da kasa, majalisar musulmin kasar Kenya ta ce ba za ta goyi bayan wani daga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar ba, tare da kiran malamai da shugabannin musulmi da su yi haka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, majalisar musulmin kasar Kenya ta ce ba za ta goyi bayan wani daga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar ba, tare da kiran malamai da shugabannin musulmi da su guji nuna goyyon baya ga duk wani dan takara.

Wannan kira ya zo ne a daidai lokacin da ake shirin sake gudanar da zaben shugaban kasa a Kenya, bayan da babbar kotun kolin kasar ta sanar da soke zaben da aka yi a kwanakin baya.

Bayanin majalisar malaman ya ce malaman addini idan suka nuna goyon baya ga wani bangare ko wani dan takara to hakan yana da tasiri ga daya bangaren, ta yadda wasu lokuta yak an jawo rikici na addini da bangaranci.

A kan majalisar musulmin ta ce dukkanin malaman addinin muslunci su bar mabiyansu su zabi wanda suke so bisa zabinsu ba tare da nuna musu goyon baya ga wani daga cikin ‘yan takara ba.

A ranar 26 ga wannan wata na Oktoba ne dai za agudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu, wanda ‘yan adawa suka ce za su kaurace masa.

3654268


captcha