IQNA

An Buga Littafin Tafsirin Imam Khomeini (RA) A Kasar Spain

23:47 - February 18, 2018
Lambar Labari: 3482405
Bangaren kasa da kasa, an buga littafin tafsirin Imam Khomeini (RA) da aka fi sani da tafsirin surat hamd a kasar Spain.

 

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na bangaren hulda da jama’a na cibiyar yada al’adun musulunci cewa, karamin ofishin jakadancin Iran ne a kasar ta Spain ya dauki nauyin buga littafin,a wani shiri na yada rubuce-rubucen da ak ayi a cikin harshen farisanci.

Wannan littafi dai Raul Gozales ne ya tarjama shi zuwa harshen spananci, kamar yadda cibiyar Fatima ta dauki nauyin bugawa, inda karamin ofishin jakadancin Iran ya bayar da dukkanin abin da ake bukata domin aikin buga wannan littafi.

An harhada bayanan da Imam Khomeini (RA) yayi na tafsirin surat Fatiha tun kimanin shekaru kafin juyin muslunci, inda daga bisani aka mayar da shi littafi.

3692610

 

 

captcha