Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na vetogate.com cewa, Ashraf Fahimi daraktan kula da harkokin gasar kur’ani a ma’aikatar harkokin adini ta Masar ya bayyana cewa, dukkanin wadanda za su shiga gasar karatun kur’ani ta duniya karo na ashirin da za a gudanar a kasar, dole ne zama suna da kwarewa a kira’oi bakawai.
Yak o shakka babu a wannan karon akwai sabbin canje-canje da za again a wannan gasa, daga ciki har da wannan tsari na samun kwarewa akan kiraoi bakawai da aka sani.
Ashraf Fahmi y ace wannan gasar za ta samu halartar wakilai daga kasashe 70 na duniya, da suka hada da na larabawa da na musulmi da kuma wasu daga yankunan turai da Asia.
Za a bayar da kyautar fan miliyan daya na Masar ga duk wanda ya yazo na daya agasar, kamar yadda kuma za abayar da wasu kyatuka na musamman ga wadanda suka zo matakai na biyu da na uku.