Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na cibiyar Imam Ali (AS) cewa, za a fara gudanar da wannan zaman ne daga gobe 20 ga watan Fabrairu.
Hottatol Islam Said Jazari shi ne zai gabatar da jawabi a wurin zaman makokin.
Babban abin da wannan taron makoki zai mayar da hankali a kansa shi ne, irin gudunmawar da wannan baiwar Allah ta bayar wajen gina al'umma mumina a kan tarbiya irin ta manzon Allah, hakuri da juriya irin na manzon Allah.
Irin tarbiya da kyawawan halaye na Fatima Zahra amincin Allah ya tabbata a gare ta, shi ne irin tarbiya da dukkanin limaman tsira na Ahlul bait (AS) suka tashi a cikinta.
Kamar yadda kuma ta zama babban abin buga misali a wajen gwarzantaka da nuna jajircewa wajen bin uamrnin Allah da manzonsa komai tsanani komai wahala ba tare da nuna karaya ba.