IQNA

Zaman Taro Kan Raya Aadun Musulunci A Kasar Masar

23:47 - February 20, 2018
Lambar Labari: 3482413
Bangaren kasa da kasa, a yau ake gudanar da zaman taron raya al’adun muslunci a kasar Masar wanda cibiyar yada al’adu ta kasar ta dauki nauyin shiryawa.

 

Kamfanin dillacin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jaridar yanar gizo na yaum sab cewa, an fara gudanar da zaman taron raya al’adun muslunci a kasar Masar wanda cibiyar yada al’adu ta kasar ta dauki nauyin shiryawa a kasar.

Wannan taro dai yana mayar da hankali ne kan muimmanci yada ala’dun muslunci ga sauran al’ummomin duniya, kasantuwar musulunci addini mai koyar da dan adam dukkanin ilimi da dabiu kyawawa ta hanya mafi dacewa da rayuwa.

Aladun musulunci dais u ne al’adun da ya koyar ko ya tabbatar da su bayan samunsu a tsakanin wasu kabilu musamman larabawan jahiliya.

3693327

 

 

 

 

 

 

 

 

 

captcha