IQNA

Cin Zarafin Al’ummar Palastinu Ba Abu Ne Da Ya Kamata A Yi Shiru Kansa Ba

23:51 - May 18, 2018
Lambar Labari: 3482669
Bangaren siyasa, Limamin da ya jagorancin sallar juma'a na nan birnin Tehran ya bayyana cewa mayarda ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin Qudus babbar masifa ce a duniya yau tun bayan kafa haramtacciyar kasar Isr'aila.

 

Hujjatul-islam wal musulimin Kazen Siddiqi limamin da ya jagoranci sallar juma'ar birnin Tehran ya bayyana mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin Qudus a matsayin abinda ya saba dokokin kasa da kasa da kuma tauye hakkokin Palastinawa a kasarsu ta haihuwa, sannan ya ce bayan da  al'ummar Palasrinu suka tashi domin bayyana rashin amincewa da wannan mataki, sai suka fuskanci mayar da martani da harshashi, inda jami'an tsaron suka kashe mutane kimanin 60 a rana guda.

Hujjatul-islam Siddiqi ya kara da cewa kisan da jami'an tsaron Haramtacciyar kasar Isra’ila  suka yi kan fararen hula da ba sa dauke da makamai bisa zalinci ya kara sanya bakin fanti a fayil din wannan Haramtacciyar kasa, da Amurka gami da masu goyon bayansu a yankin.

A yayin da yake ishara kan yadda Palastinawa ke cikin tsananin kangi na zalincin hukumomin Haramtacciyar kasar Isra’ila  masu shan jinin kananen yara, hujjatul-islam Siddiqi ya ce duk da irin adawa da al'umma da kuma hukumomin kasashen Duniya ke nunawa kan wannan ta'addanci, to amma abin bakin ciki wasu kasashen larabawan yankin dake karkashin mamayar Amurka da kasashen yamma gami da Haramtacciyar kasar Isra’ila  sun yi shuru da bakunansu.

Limamin ya tabbatar da cewa wannan ta'addanci da hukumomin Haramtacciyar kasar Isra’ila  ke yi kan al'ummar Palastinu ya nuna cewa karshen wannan haramtaccen milki na zalinci ya kusa.

3715481

 

 

captcha