Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya kasar Paraguay ta bude ofishin jakadancinta a hukumance a birnin Quds mai alfarma domin amincewa da wannan birni a matsayin babbar birnin haramtacciyar gwamnatin yahudawan Ira’ila.
Jaridar Albayan ta kasar hadaddiyar daular larabawa ta rubuta cewa, tun bayan da Amurka ta bude ofishin jakadancnta a makon da ya gabata, lamarin yake ci gaba da fskantar tofin Allah sine a duniya, da kuma tsakanin al’umma Palastinu, wadanda Isra’ila ta kasha kimanin mutane 65 daga cikin a kasa watanni biyu, wadanda suke nuna rashin amincwa da mama kasarsu.
A ranar Laraba da ta gabata ma kasar Guatimala ta mayar da nata ofishin jakadancin zuwa Quds, tare da halartar shugaban kasar Jimmy Morales.