IQNA

Sojojin Myanmar Sun Kashe Wani Matashi Musulmi

22:51 - January 16, 2019
Lambar Labari: 3483319
Sojojin gwamnatin kasar Myanamar sun kasha wani matashi musulmi tare da jikkata wasu ba tare da sun aikata wani laifi ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, matasa uku ne suka tafi domin samo ma iyayensu itace girkia  cikin dajin da ke kusa da su a kauyen Busid Wang a cikin lardin Rakhin, amma kwanaki biyu matasan ba su dawo ba.

Bayan bin diddigin lamarin an gane cewa sojojin gwamnatin kasar ta yanamr ne suka harbe da su da bindiga, amma sojojin sun ce hakan ya faru ne bisa kure.

Sojojin suka kara da cewa a lokacin da suka ga matasn sun sun bukaci su mika kansu, amma suka ji tsoro suka ruga, saboda haka suka bude wuta a kansu, kuma daya daga cikin matasan ya rasa ransa, biyu kuma sun samu munanan raunuka.

Wannan dai na zuwa ne  adaidai lokacin da gwamnatin kasar ta Myanmar da jami'an sojinta suke da'awar cewa suna son zaman lafiya tsakaninsu da musulmin kabilar Rohingya, da kuma neman wadanda suka yi gudun hijira da su dawo gida.

A cikin shekaru biyu zuwa uku da suka gabata ne dai jami'an sojin gwamnatin Myanmar tare da 'yan addinin buda masu tsattsauran ra'ayi suka yi kisan kiyashia  akan dubban musulni 'yan kabilar Rohingya na kasar, lamarin da ya sanya fiye da mutane dubu dari shiga na 'yan kabilar Rohingya suka yi gudun hijira zuwa kasar Bangaladaesh da ke makwabtaka da su.

3781802

 

 

captcha