IQNA

Kamfe Na Kaurace Wa Sayen Kayan Isra'ila A Ingila

23:56 - May 17, 2019
1
Lambar Labari: 3483649
Bangaren kasa da kasa, musulmin kasar Birtaniya sun kaddamar da wani kamfe na kaurace wa sayen kayan Isr'ila musamman dabino a cikin wannan wata na Ramadana.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na cibiyar IHRC a kasar Birtaniya ya bayar da rahoton cewa, cibiyar kare hakkokin musulmi a kasar Birtaniya, ta kaddamar da kamfe na kauracewa sayen kayan Isra'ila musamman dabino da muuslmi suke yawan yin amfani da shi a cikin wannan wata fiye da sauran lokuta.

Mas'ud Shajar bababban sakataren IHRC ya ce, yana da kyau al'ummar Birtaniya su kaurace wa wadannan kaya, domin kuwa ana samar da su ta hanyar mamaya da zalunci.

Ya kara da cewa, Isra'ila tana fitar da dabino na kimanin fan miliyan 151, amma na kimanin fan miliya 23 ana sayar da shi ne a Ingila.

Kimanin kashi sattin na dabinon da sra'ila take nomawa dai tana noma shi ne  a cikin yankunan falastinawa da ta mamaye.

A cikin shekara ta 2005 n wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama 170 suka kaddamar da kamfe mai take a kaurace wa kayan Isra'ila, daga bisani kuma ya samu karbuwa a duniya.

 

3811956

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
ibrahim musa
0
0
kaurace ma israila,da kayanta wajibine dukkan musulmi.
captcha