IQNA

Sabon Shugaban Tunisia Ya Kare matsayinsa Dangane Da Palastine

23:24 - October 14, 2019
Lambar Labari: 3484153
Sabon shugaban kasar Tunisia ya kare matsayinsa dangane da yadda yake bayar da muhimmanci ga batun palastine.  

Kamfanin dillancin labaran iqna, a jawabinsa na farko bayan kada kuri’a  a jiya, Qais Sa’id sabon zababben shugaban kasar Tunisia ya kare matsayinsa dangane da yadda yake bayar da muhimmanci ga batun palastine da kuma wajabcin kare al’umarta.

Ya ce batun palastine batu ne ‘yan adamtaka a mataki na farko, wanda ya hada dukkanin mutanen duniya, musulmi da wanda ba musulmi ba, sannan kuma ga musulmi da larabawa batu ne na asasi, wanda a halin yanzu shi ne abbabr matsalarsu da ke ci musu tuwo a kwarya.

Tun a lokacin yakin neman zabe Qais said ya tabbatar ad cewa idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasar Tunisia ba zai taba kulla alaka da Isra’ila ba.

Dubban mutanen kasar Tunisia sun fito kan tituna suna daga tutar kasar don nuna farin cikinsu da zaben Kais Sa’ied a matsayin shugaban kasa a zaben da aka gudanar a jiya Lahadi.

Mutanen kasar a birnin Tunis babban birnin kasar sun rufe wani babban titi a birnin mai suna Titin Habib Bogiba suna ta nuna farin cikinsu da sakamakon zaben wucin gadi wanda ya nuna cewa Kais Sa’id yana kan gaba da kimanin kashi sabain da bakawai cikin dari na kuri’un da aka kada a zabe.

Kais Saed dai dan takarar shugaban kasa ne a zaben na jiya, amma wanda bai da jam’iyya, kuma shi ne a gaba a zaben zagaye na farko wanda aka gudanar a cikin watan da ya gabata, sannan a zagaye na biyu wanda aka gudanar a jiya Lahadi 13 ga watan Oktoba, yana kan gaba, duk fa cewa kwamitin zaben kasar bata bayyana cikekken sakamakon zaben gaba daya ba.

3849785

 

 

 

captcha