IQNA

Za A Gurfanar Da Sheikh Zakzaky A Gaban Shari’a

22:57 - December 21, 2015
Lambar Labari: 3467974
Bangaren kasa da kasa, rahotanni daga Najeriya sun za a gurfanar da jagoran mabiya mazhabar shi’a a gaban kuliya domin hukunta shi.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Press TV cewa, gwamnan jahar Kaduna Nasir Elrufai ya bayyana cewa suna shirin gurfanar da sheikh Ibrahim Zakzaky a gaban kuliya domin hukunta shi kana bin da ya faru a cikin makon da ya gabata.

A cikin wani bayani da ya gabatar bayan kisan gilla da sojojin kasar suka yi kan mabiya mazhabar shi’a a garin Zaria, gwamnan jahar ya fito ya bayyana cewa jagoran yan shi’a da mabiyansa su ne ke da laifi.

Ya kara da cewa yanzu haka sun riga sun kafa tawaga wadda za ta jagoranci gabatr da sheikh a gaban kuliya domin hukunta, kamar yadda kuma ya bayyana cewa sun kafa wani kwamiti dominciken abin da ya faru.

Tun a cikin makon da ya gabata ne dai jami’an sojin gwamnatin Najeriya suka kaddamar da hari da manyan makamai da bam a kan yan shi’a da bas u dauke da wani makami, inda aka kashe adadi mai yawa daga cikinsu.

Har yanzu babu wanda ya san adadin mutanen ad sojoji suka kashe abin da ya faru, duk kuwa da cewa wadanda suka ganewa idanunsu abin da ya faru suna cewa adadin yah aura dubu daya.

Mabiya mazhabar shi’a sun ce ba za su taba amincewa da abin da kwamitin gwamnati zai fitar ba, domin kuwa zai dogara ne kawai da abin da sojoin da suka yi kisan kan za su ambata.

3467578

Abubuwan Da Ya Shafa: nigeria
captcha