Kamfanin dillancin labaran Anadolu ya bayar da rahoton cewa, a yayin da yake gabatar da jawabi a gaban taron Palestine a birnin Kualalampour, Mahatir Muhammad firai ministan rikon kwarya ya bayyana cewa, manyan kasashen duniya suna kauda kansu daga zalincin da yahudawa suke tafkawa a kan falastinawa.
Ya ce a duk lokacin da aka yi magana da al’ummar Falastinu da kuma zaluncin da yahudawan Isra’ila suke yi musu, sai manyan kasashen duniya su bata rai, tamkar cewa su Falastinawa ba mutane ba ne da suka cancanci su rayu kamar kowa.
Ya ci gaba da cewa, ko da wasa kasarsa ba za ta taba canja matsayinta na nuna cikakken goyon baya ga al’ummar falastinu ba, kamar yadda kuma za ta ci gaba da nuna adawa da duk wani mataki na danne hakkokinsu da zaluntarsu.