IQNA

Gasar Kur’ani Ta Hanyoyi Na Digital Ta Afirka A Masar

23:52 - April 22, 2020
Lambar Labari: 3484733
Tehran (IQNA) za a gudanar da gasar kur’ani ta hanyoyi na zamani ta digital da aka saba gudanarwa ta Afrika  a kasar Masar.

A cikin wani bayani da kafofin yada labaran kasar Masar suka bayar kan batun, Hussain Abul Ata shugaban hukumar raya al’adu da bunkasa yawon bude ido kan lamurra da suka shafi kur’ani a Masar ya bayyana cewa, za  agudanar da gasar kamar yadda aka saba, amma a wanann karo ta hanyoyin sadarwa ne kawai ba tare da halartar jama’a ba.

Ya ce za a nuna ci gaba  da aka samu a bangarori na ilimin kur’ani mai tsarki ta hanyoyin na zamani da syuka hada na’ura mai kwakwalwa, da sauran shirye-shirye wadanda aka tanada a cikin ababen ajiye hotuna ko sauti ko hotuna masu motsi, na bidiyo da makamantansu.

Gasar dai za ta samu halartar mutane da dama daga kasashen Afirka ta hanyar yanar gizo, bayan da suka aiko da abubuwan ad suka tanada ga zuwa ga ofishin cibiyar da ke kasar masar, inda a cikin watan Ramadan ne za a fara nuna abubuwan da jama’a suka tura na gasar.

Daga karshe kuam za a sanar da sunayen wadanda suka lashe gasar da kuma kasashensu, da kuam irin kyautuka da za a ba su.

3893502

 

 

captcha