IQNA

Haramta ayyukan siyasa a masallatai a jihar Johor, Malaysia

15:59 - February 19, 2022
Lambar Labari: 3486958
Tehran (IQNA) An hana gudanar da harkokin siyasa da na zabe a masallatai da wuraren ibada a jihar Johor ta kasar Malaysia.

Kamar yadda shafin jaridar The Star ya ruwaito, shugaban kwamitin kula da harkokin addini na gwamnatin jihar Johor, Toussaint Jarwanti, ya ce sashen kula da masallatai da wuraren addinin musulunci na sashen kula da harkokin addinin musulunci na jihar ne suka yanke wannan shawarar.
Ya kara da cewa hakki ne da ya rataya a wuyan jami’an jihar su tabbatar da cewa ba a yi amfani da masallatai da wuraren addinin musulunci a jihar a matsayin wurin gudanar da harkokin siyasa daga shugabannin jam’iyyu ba.
Ya ce: "Babu wani daga cikin shugabannin siyasa, hatta jami'an gwamnati da aka yarda ya yi amfani da masallatai da wuraren Musulunci wajen gudanar da harkokin siyasa."
Hukumar zaben jihar Johor ta ware ranar 26 ga watan Fabreru a matsayin ranar tantancewa da kuma ranar 12 ga watan Maris a matsayin ranar zaben jihar.
 
 
https://iqna.ir/fa/news/4037199
 

Abubuwan Da Ya Shafa: malaysia jihar Johor
captcha