IQNA

Wani dan kasar Yemen ya lashe kyautar haddar kur'ani ta kasa da kasa a kasar Kuwait

16:17 - October 20, 2022
Lambar Labari: 3488042
Tehran (IQNA) Wani dan kasar Yemen ya lashe matsayi na daya a gasar haddar Alkur'ani da aka gudanar a kasar Kuwait.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Shamahed Net cewa, Al-Hafiz Abu Bakr Ali Ahmad Al-Dzabi ya ce dangane da gasar da ya halarta: Wannan gasar kur'ani mai tsarki ta kasance gasa ce ta duniya inda sama da mahalarta 175 da suka wakilci kasashe sama da 70 suka halarta.

Al-Dzabi ya kara da cewa: Wannan gasar ta kunshi bangarori da dama na ilimomin kur'ani mai tsarki, musamman ma shahararriyar ruwayar Hafsu daga Asim, wadda ta zama ruwan dare a kasashen Larabawa da na Musulunci da dama.

Al-Dzabi ya kara da cewa gasar haddar kur’ani mai tsarki da karatun kur’ani goma tana da matukar wahala, kuma a dalilin haka mutane kasa da 20 ne suka samu shiga gasar.

A watan Oktoban bana, wani dan kasar Yemen mai suna Ebrahim Ahmed Aljundi ya lashe matsayi na daya a gasar irin wannan da Turkiyya ta dauki nauyin shiryawa tare da halartar mahalarta 66 daga kasashe fiye da 50.

 

4093097

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: bangarori ilmomi kasashen rayuwar gasa
captcha