IQNA

Kyakkyawar tarba ga makarancin kur’ani na Masar a Bangladesh

17:46 - March 06, 2023
Lambar Labari: 3488763
Tehran (IQNA) Dubban jama'a ne suka yi maraba da karatun kur'ani mai tsarki da Mahmoud Kamal al-Najjar ya yi a birnin Ghazipur na kasar Bangladesh.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Watan cewa, karatun kur’ani mai tsarki na Mahmud Kamel al-Najjar, wani makarancin kasar Masar ya samu tarba daga dubban jama’a a birnin Ghazipur na kasar Bangladesh.

An gudanar da wannan taro na kur’ani ne a matsayin taron ‘’yan kungiyar Iqra’ karo na 22 musamman na kur’ani mai tsarki da ke shirya tarukan kur’ani a duk shekara a garuruwa daban-daban na kasar Bangladesh.

Mahmud Kamel al-Najjar, wani makarancin kasar Masar da ya kammala tafiyarsa ta kur'ani a lardin Daqahlia na kasar Masar ya bayyana cewa: Na yi mamakin kasancewar dimbin masu sha'awar karatun kur'ani mai tsarki. A cewarsa, duk da ziyarar da ya yi zuwa kasashen Musulunci da na Larabawa daban-daban, bai taba ganin irin wannan liyafar karatun Alkur’ani ba.

Mahmoud Kamel al-Najjar ya fara karatun kur'ani mai tsarki a da'irar kur'ani a kasashe daban-daban bayan ya kammala karatunsa a jami'ar Azhar. Ya zuwa yanzu dai Al-Najjar ya yi tafiya zuwa kasashe irin su Pakistan, Kuwait, Turkiyya, Indiya da Bangladesh. Sai dai ya fayyace cewa: Abin da na gani a kasar Bangladesh ya sha bamban da sauran kasashen duniya wajen karbar karatun kur’ani da mutane ke yi.

 

استقبال بی‌نظیر از قاری مصری در بنگلادش+ عکس

استقبال بی‌نظیر از قاری مصری در بنگلادش+ عکس

استقبال بی‌نظیر از قاری مصری در بنگلادش+ عکس

استقبال بی‌نظیر از قاری مصری در بنگلادش+ عکس

استقبال بی‌نظیر از قاری مصری در بنگلادش+ عکس

استقبال بی‌نظیر از قاری مصری در بنگلادش+ عکس

 

 

 

4126330/

 

 

captcha