IQNA

Sudan Ta Mika Wasu ‘Yan Kungiyar Muslim Brotherhood Ga Masar

23:01 - May 07, 2020
Lambar Labari: 3484773
Gwamnatin kasar Sudan ta mika wasu mambobin kungiyar Muslim Brotherhood ga gwamnatin kasar Masar bayan da ta kame sua  cikin kasarta.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, jami’an tsaron kasar Sudan sun mika wasu daga cikin ‘yan kungiyar Muslim Brotherhood ‘yan kasar Masar da suke zaune a  cikin Sudan bayan kame su, tare da mika su ga gwamnatin kasar ta Masar.

Daga cikin wadanda aka mika har da wasu manyan kusoshi 5 na (Sawa’id Misr) bangaren soji na Muslim Brotherhood, wadanda gwamnatin Masar take nemansu ruwa a jallo.

Jaridar Al-ittihad ta kasar UAE ta rubuta cewa, ‘yan kungiyar Muslim Brotherhood suna kyakkyawar alaka da gwamnatin Sudan a lokacin mulkin hambararren shugaban kasar Umar Hassan Albashir, amma bayan da sojoji suka karbi mulki, sun ta kama ‘ya’yan kungiyar suna mika su ga gwamnatin Masar.

Gwamnatin sojin ta Sudan ta bayyana cewa, bayan faduwar Albashir, an kame ‘yan kungiyar Muslim Brotherhood da dama da suka shigo Sudan, suna hankoron zuwa kasar Turkiya.

3897053

 

captcha