IQNA

Gwamnatin Gambia Ta Sanar Da Ashura A Matsayin Ranar Hutu A Hukumance A Kasar

22:06 - August 13, 2021
Lambar Labari: 3486199
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar Gambia ta sanar da ranar Ashura a matsayin ranar hutu a hukumance a fadin kasar.

Jaridar The Point ta bayar da rahoton cewa, a yau shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya sanar da ranar 10 ga watan Muharram wato ranar Ashura wanda zai kama a ranar Alhamis mai zuwa a matsayin ranar hutu a hukumance a fadin kasar.

Shugaban kasar ta Gambia ya ce, baya ga kasancewar ranar Alhamis tana ce ta Ashura, haka nan kuma ta yi daidai da ranar 16 ga watan Agusta, ranar da mabiya addinin kirista suke girmamawa,a  matsayin cewa a ranar ne ruhin Sayyid Maryam (AS) ya tafi sama.

Shugaba Adama Barrow ya ce har kullum musulmi da kirista suna rayuwa cikin zaman lafiya da kwanciya hankali da fahimtar juna da kuma girmama a kasar Gambia, wanda a cewarsa wannan babban abin alfahari ga daukacin al'ummar kasar.

Kimanin kashi 95% na mutanen kasar Gambia dai musulmi ne, galibinsu kuma mabiya darikar Tijjaniya ne.

 

3990434

 

 

 

 

captcha